Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

A Filato hukuma ta haramta sayar da man fetur a bayan fage


Mutane na sayen man fetur cikin jarkoki domin su sayar a kasuwar fage da tsada
Mutane na sayen man fetur cikin jarkoki domin su sayar a kasuwar fage da tsada

Jami'an tsaro a jihar Filato sun baiwa 'yan bumburutu da masu sayar da man fetur ba bisa ka'ida ba wa'adin awa ishirin da hudu su san inda dare ya yi masu ko su fuskanci fushin hukuma

Kakakin rundunar tsaron ta musamman a jihar Filato Keften Ikedishi Iweha yace hukuma ta dauki mataki haramta sayar da man fetur a kasuwar bayan fage domin tabbatar da wadatar man da kuma hana bata gari damar aiwatar da wasu mugayen aiki.

Keften Iweha yace na farko dai sun dauki mataki ne domin umurni suka samu daga sama. Na biyu ayyukan 'yan bumburutu na hana jama'a samun mai da sauki. Abu na uku suna sayar da man da tsada lamarin da ya hana mutane cin moriyar kudinsu.

Yace yawancin wadanda suke sayar da man fetur ta bayan fage akwaisu da wasu ayyuka mara kyau musamman can cikin dare. Sun sha samunsu a wuraren da ake sata da fashi da wasu ayyukan barna. Da zara karfe goma sha biyu ta wuce sai kuma su shiga shaye-shaye.

Wasu da aka tarardasu a dogon layi inda suke jiran sayen mai sun tofa albarkacin bakinsu bisa sabon matakin da jami'an tsaro suka dauka. Wani Wale Akanji yace a gaskiya masu kasuwar bayan fage suna hana mutane samun mai a gidajen man fetur. Banda haka suna hada kanazir da man fetur su sayarwa mutane.

Matsalar karancin man fetur ta kazance inda 'yan bumburutu ke sayar da galan daya nera dubu ko fiye da haka.

Ga karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:19 0:00

XS
SM
MD
LG