Kungiyar kwadago a Najeriya NLC, ta yi kira ga shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, da ya tabbatar da an hanzarta aiwatar da biyan albashi mafi karanci a kasar.
A cewar, kungiyar wacce ta bayyana hakan a wata sanarwa da ta wallafa a shafinta na Twitter a jiya juma’a, dauke da sa hannu Sakatare Janar dinta, Dr. Peter Ozo-Ezen, “muna yabawa shugaban kasa” da ya sanya hannu a dokar, amma akwai bukatar a ga an hanzarta biyan albashin.
“Muna amfani da wannan dama, domin mu yi kira da a gaggauta aiwatar da wannan doka, lura da cewa an jima ana ja-in-ja har na tsawon kusan shekaru biyu.”
Kungiyar ta kara da cewa, “muna kira, musamman ga gwamnatin tarayya da jihohi, da su gaggauta tattaunawa da kungiyoyi masu ruwa da tsaki, kan tasirin da wannan sabuwar doka za ta yi,” a matattakalar biyan albashi.
A ranar Alhamis din da ta gabata ne, shugaba Muhammadu Buhari ya sanya hannu a dokar karin albashi mafi karanci a Najeriyar.
Za ku iya son wannan ma
-
Janairu 27, 2023
‘Yan Najeriya Sun Yi Barazanar Yin Bore Kan Wa'adin Canjin Kudi
-
Janairu 27, 2023
Ba Wanda Zai Yi Asarar Kudinsa Idan Na Hau Mulki – Kwankwaso