Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

A Jamhuriyar Nijar Mutane Kusan Miliyan Biyu Ne Ke Bukatan Taimakon Gaggawa


Shugaban Nijar Issoufou Mahamadou

A wannan shekara ta dubu biyu da goma sha bakwai kimanin mutane miliyan daya da dubu dari tara ke bukatan taimakon gaggawa a Jamhuriyar Nijar inda jihar Diffa kadai tana da irin wadannan mutanen miliyan daya da dubu dari uku da arba'in

Daga cikin muhimman fannonin da ake bukatar agaji sun hada da abinci da mutane miliyan daya da dari uku ke bukata cikin gaggawa.

Kimanin kashi hamsin na mutanen mata ne dake yaki da tamowa dake bukatan abinci mai gina jiki. Mafi yawansu yara ne da suke fama da karancin abinci, 'yan kasa da shekaru goma sha takwas.

Akwai kuma wadanda annoba ta samesu tare da ambaliyar ruwa da kuma 'yan cirani.

Ali Aba shugaban kungiyar agaji a jihar Diffa yace jihar gaba daya na iya fadawa cikin yunwa saboda kusan shekara daya ke nan da ba'a yi noma ba saboda dalilai na tsaro.Yace kodayake gwamnati tana kokarinta amma abun da ake samu bai isa ba. Kamata yayi a kara.

Wata kungiayr kuma dake aiki a Diffan ta bakin jami'inta Ali Zuberu tace tayi harama inda take anfani da kidigdigan da aka yi domin samun agaji.

Ga rahoton Tamar Abari da karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:54 0:00

Gobara A Jihar New York

An Yi Jana'izar Mutane 15 Da Suka Mutu A Gobara A Jihar New York
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:00 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Sauyin yanayi : Yankin Sahel na Afrika

Yadda Sauyin Yanayi Ke Rura Wutar Rikici A Yankin Sahel
please wait

No media source currently available

0:00 0:12:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Nijar, Fulani, Wodaabe

Yadda Funalin Wodaabe Suka Gudanar Da Gasar Nuna Kyau A Nijar
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:22 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG