Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

A jamhuriyar Nijar 'yansanda uku sun rasa rayukansu cikin harin da aka kaimasu


Shugaba Mahamadou Issoufou na Jamhuriyar Nijar
Shugaba Mahamadou Issoufou na Jamhuriyar Nijar

Wasu ‘yan sanda uku sun rasa rayukansu bayan wani hari da aka kai kan jami’an kasar Jamhuriyar Nijar a kan iyakar kasar da Najeriya da Burkina Faso da kuma Mali.

Ma’aikatar tsaron kasar ce ta fitar da wata sanarwa ta kafar talbijin, inda Kanar Ledru Moustapha ya bayyana cewa wasu mahara akan babura hudu da wata mota kirar Toyota suka kai harin.

A wani hari na daban, wasu dakarun kasar ta Nijar sun samu raunuka yayin da wasu masu harin kunar bakin wake su biyar suka mutu a wani harin kwantan-bauna da aka kai a yankin Diffa, harin da hukumomin kasar suka dora alhakinsa akan mayakan Boko Haram.

Wadannan hare-hare- na zuwa ne a daidai lokacin da kasar ta Nijar ke shirin yin zaben shugaban kasa a zagaye na biyu.

Wani kakakin bangaren ‘yan adawa, Amadou Bjibo, ya yi kira ga masu kada kuri’a da su kauracewa zaben, domin a cewarsa zaben da aka yi ranar 21 ga watan Farbrairu yana cike da kura-kurai.

Hawan Nasarawa, jihar Kano a Najeriya, lokacin da aka gudanar da bukukuwan Sallar Eid el Fitr
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG