Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

A Jamus mutum daya ya rasa ransa sanadiyar fashewar wani abu


Motar da fashewar wani abu ya rutsa da ita da matukinta a Jamus

A Jamus mutum daya ya mutu da safiyar yau Talata a babban birnin kasar, sakamakon wata fashewa wani abu a cikin wata mota, lokacinda jama'a suke ribibin tafiya bakin aiki.

Mukaddashin Kakakin Rundunar 'Yansandan Berlin, yace masu bincike suna aiki bisa zaton cewa wani abun fashewa ne a cikin motar ko daga waje ne ya haddasa fashewar data kashe matukin motar.

Kakakin 'Yansandan yace har yanzu masu bincke suna kokarin su tantance ko wanene mutumin, kuma suna duba ko wane banagare danagne da al'amarin.

Babu wanda ya jikkata sakamakon fashewar duk da cewa akwai yawan zirga zirgan mutane a lokacinda lamarin ya auku.

'Yansandan birnin sun killace yankin baki daya, suka shawarci mazauna unguwar su zauna cikin gidajensu kuma su rufe tagoginsu, har sai sun sami karin umarni daga hukumomin kasar, domin suna ci gaba da bimcike domin tabbatar d a cewa babu wasu fashe fashe da basu tashi.

Motar da ta tarwatse sanadiyar tashin wani abu wanda ya halaka matukinta
Motar da ta tarwatse sanadiyar tashin wani abu wanda ya halaka matukinta

XS
SM
MD
LG