Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

A Turkiya wani mummunan harin kunar bakin wake ya kashe mutane 126


Barnar da kunar bakin wakenya haddasa
Barnar da kunar bakin wakenya haddasa

A yau Litinin jami’an tsaro a Turkiyya sun ce wata mata daga bangaren Kurdawa, na daga cikin mutane biyun da ake zargi da kai mummunan harin kunar bakin waken da ya halaka mutane 37 a Ankara, kana ya jikkata wasu 125.

Hukumomin kasar dai ba su ambaci sunan matar ba, amma sun ce an haife ta ne a shekarar 1992, ta kuma zauna a gabashin birnin Kars da ke Turkiyya, sannan daga baya ta shiga kungiyar PKK da aka haramta a shekarar 2013.

Wannan hari da aka kai ranar Lahadi a dandalin Kizilay da ke Ankara, an kai shi ne a wani babban wajen hada-hadar kasuwanci da sufuri, kuma shi ne na biyu mafi muni a jerin hare-haren da aka kai a watan da ya gabata, wanda hukumomin kasar ke dora alhaki akan mayakan Kurdawa.

Su dai mayakan na Kurdawa sun kwashe shekaru kusan 30 suna fada da dakarun kasar a wani mataki na neman ‘yancin kansu a kudu maso gabashin kasar.

Akalla mutane 210 suka rasa rayukansu a hare-haren kunar bakin waken da ake zargin kungiyar ta mayakan Kurdawa ko kuma mayakan IS da kaiwa.

A halin da ake ciki yanzu, Shugaban kasar ta Turkiyya Recep Tayyip Erdogan, ya sha alwashin ganin bayan duk wata kungiyar ‘yan ta’adda na kasar.

Bayan mutane 126 sun mutu da dama sun jikata ana kuma kwashesu zuwa asibiti
Bayan mutane 126 sun mutu da dama sun jikata ana kuma kwashesu zuwa asibiti

XS
SM
MD
LG