Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

A Jihar Adamawa Shugabannin Musulmi da Kirista Suka Yi Taron Neman Zaman Lafiya


Jihar Adamawa

A wani yunkurin tabbatar da zaman lafiya da magance banbance banbance tsakanin Musulmi da Kirista a jihar Adamawa kungiyoyin addinan biyu sun gudanar da wani taron sirri a Yola don gano bakin zaren kawo fahimtar juna a jihar.

Cikin kwanakin nan dai rayuka da dama ne suka salwanta a wasu jihohin Najeriya,sakamakon tashe tashen hankulan da ake samu da sau tari kan rikide su koma fadan kabilanci ko addini,lamarin da kan jawo asarar rayuka da kuma dukiya.

Jihar Adamawa na cikin irin wadannan jihohi,kuma don magance wannan matsalar ce ma,yasa hadakar majalisar kungiyar addinan Musulunci ta Muslim Council da kuma ta Kristocin Najeriya reshen jihar shirya wani taron sirri na gano bakin zaren samun fahimtar juna a tsakanin mabiya addinan biyu.

Mallam Sahabo Magaji shi ne shugaban majalisar hadinkan Musulmi a jihar ta Muslim Council ,yace a taron nasu sun tattauna ne kan matsalolin dake tasowa yanzu,da akan danganta da addini.

To ko wane tasiri taron ke da shi wajen samar da zaman lafiya a jihar? Bishop Steven Dami Mamza shi ne shugaban kungiyar Kiristoci ta kasa,CAN, reshen jihar Adamawa, yace dole jama’a su fahimci muhimmancin zaman lafiya.

Ana dai sa ran wannan taro dake zama irinsa na farko zai taimaka,wajen shawo kan banbance banbancen kabilanci da na addini a jihar.

A saurari rahoton Ibrahim Abdulaziz da karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:44 0:00

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG