Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Taron Kolin Kasa Ya Tattauna Game Da Hanyoyin Magance Matsalar Tsaro


Tsoffin Shugabannin Najeriya
Tsoffin Shugabannin Najeriya

An kammala taron kolin kasa inda aka tattauna game da manya-manyan matsalolin tsaro, da suke damun ciki da wajen Najeriya.

Taron kollin tsaro na kasa ya samu halarcin shugaban kasa Muhammadu Buhari, gwamnoni 36, tare da tsofaffin shugabanin kasa, da ya kuma hada da alkalin alkalai, kana shugaban majalisar dattawa da na wakilai.

Gwamnan jihar Jigawa Abubakar Badaru, ya zanta da manema labarai, inda ya bayyana abubuwan da suka tattauna akai, da suka hada da matsalar tsaro, da ta shafi satar jama’a da garkuwa da su, da rikici tsakanin manoma da makiyaya, haka kuma da matsalar tsagerun Naija Delta.

Ya bayyana cewar mai ba shugaban kasa shawara a harkar tsaro ya kwashe tsawon lokaci yana gabatar da bayanan matakin da suke dauka, da kuma shawarwari da masana harkar tsaso su ke badawa don ganin an magance matsalar a kowane mataki.

A cikin jawaban da aka tattauna, an karfafa magana akan matsalar yadda ake ma Fulani kallon wadanda ba ‘yan kasa ba, bayan sun kwashe shekaru a yankunan da suke, wannan shima matsala ce da su ka tatauna yadda za’a bullo da hanyar magance ta.

A karshe dai taron ya tattauna kan hanyoyin da za a bi don kyautata danganta tsakanin ‘yan kasa na kowane yanki, kabila, da addinai, da mutunta juna, kana an dauki matsaya daya da ta shafi tattalin arzikin kasa.

  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jarida da ke aiki da Sashen Hausa na Muryar Amurka (VOA). Yana da kwarewa a fannoni da dama, da suka hada da shafukan yanar gizo, talabijin, bincike, rubutu da hotuna. Dan asalin kauyen Hiliya ne daga karamar Hukumar Tambuwar a jihar Sakkwato.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG