Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gwamnatin Jihar Kaduna Ta Kafa Dokar Hana Fita A Kafanchan Tun Ranar Alhamis


Sojojin Najeriya.
Sojojin Najeriya.

Sakamakon rikici da ya barke tsakanin musulmi da kirista a kafanchan a kudancin Kaduna, ya sa gwamnati ta kafa dokar hana fita sam sam.

Sakamakon barkewar rikici tsakanin musulmi da kirista a kafanchan, lamari da ya haifarda zaman dar dar, gwamnatin jihar kaduna ta kafa dokar hana fita a yankin tun ranar Alhamis.

Duka sassan biyu suna zargin juna da tada fitinar wacce tayi sanadiyyar hasarar rayuka daga duka sassan biyu. Zuwa yanzu dai babu adadin mutane d a suka halaka sakamaon wannan rikici.

Mazauna yankin suna kira ga gwamnatin jihar ta sassauta dokar hana fita d a ta kafa saboda mutane suna fuskanatar karancin abinci da wasu muhimman kayan more rayuwa. Wannan dokar tuni ta hana mutane zuwa ayyuakan ibada ranar jumma'a da kuma lahadi.

Injiniya Sa'ad Bako mai gyaran na'ura mai kwakwalwa yace lamarin yana da dan sauki a unguwarsu, domin suna fita su zauna idan suka hangi jami'an tsaro sai su koma cikin gida. Yace ba haka lamarin yake a wasu unguwanni ba.
Mr. Joel shugaban matsa na kungiyar CAN ya yaba d kafa dokar hana fitar, duk haka shi ma yana kira da gwamnati ta sassauta dokar.

please wait

No media source currently available

0:00 0:07:48 0:00
Shiga Kai Tsaye
XS
SM
MD
LG