Accessibility links

Wasu 'Yan Majalisar Dokokin Najeriya Sun Yi Tur Da Harin Abuja

  • Garba Suleiman

'Yan sandan hukumar tsaron cikin gida ta Najeriya

Sanata Sahabi Ya'u da wasu 'yan majalisar sun ce akwai bukatar daukar matakan gaggawa don kawo karshen wuce-gona-da-irin da masu tsaron kasa keyi

Wasu 'yan majalisar dokokin Najeriya sun bukaci da a dauki matakai cikin gaggawa na kawo karshen cin zarafi da wuce gona da irin da wasu daga cikin mutanen da aka damkawa hakkin tsaron lafiyar kasa da al'ummarta suke yi da sunan tsaro.

Wadannan 'yan majalisar dokokin, wadanda suka je daukar gawarwakin wasu 'yan mazabunsu da aka bindige har lahira makon da ya shige a wani gidan share-ka-zauna dake dab da unguwar 'yan majalisa a Abuja, sun ce sau da dama ana hallaka mutane ko tozarta su, sai a kewaya a makala musu sunan Boko Haram.

Sanata Sahabi Ya'u daga Jihar Zamfara, wanda ya nuna katin shaida na wani dan mazabarsa daga Jihar Zamfara matukin keken-NAPEP, wanda kuma aka bindige har lahira, yace hakki ne na duk wani wanda yake da alhakin tsaron kasa a Najeriya, ya tashi tsaye domin ceto kasar daga inda ta nufa, "domin irin wadannan masifu da suke wakana, ba za a taba barinsu su na tafiya yadda suke abkuwa ba."

Sanata Sahabi Ya'u ya ci gaba da cewa, "a je a samu mutane, mutum ya kwanta da daddare yana barci, a ce wanda ya kamata ya tsare mutuncinsa, ya tsare rayuwarsa, ya tsare dukiyarsa, shi ne zai zo ya kai masa farmaki da sunan wani abu wanda ba shi ba, a hallaka mutane, a kashe su da sunan hukuma, sannan a ce musu Boko Haram, wane irin Boko Haram?"

Sanatan yace wadannan mutane su na da sana'a, su na kuma da shaidar cewa su na da sana'ar babu ruwansu da wani abu wai shi Boko Haram. Yace zasu dauki wannan batu zuwa gaban majalisa. dmin su na da yakinin cewa mutanen da aka kai musu farmakin nan ba 'yan Boko Haram ba ne.

Shi ma dan majalisar wakilan tarayya, Badamasi Dambatta daga Jihar Kano, wanda yaje karbar gawarwakin wasu daga mazabarsa da aka kashe a farmakin, a fusace, ya bayyana cewa zasu bi diddigin wannan maganar, domin bai kamata a ce a kasa kamar Najeriya wani dan kasa zai kwanta yana zullumin ko zai iya tashi lafiya saboda yana tsoron hukuma ba.

Sai kuma Amiru Tukur Nadabo, dan majalisar wakilai daga Jihar Katsina, wanda bai samu tattauna da wakiliyarmu ba, amma kuma ya karbi gawarwakin mutane 4 da aka kashe domin kaiwa gida a yi musu jana'iza a can.

Ga bayanin wadannan 'yan majalisa, da ma wasu da aka rutsa da su a cikin rahoton da Madina Dauda ta aiko.

XS
SM
MD
LG