Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

A Kamaru Iyayen Yaran Bangaren Masu Anfani da Ingilishi Na Hanasu Zuwa Makaranta


Shugaban Kasar Kamaru Paul Biya
Shugaban Kasar Kamaru Paul Biya

Ministan yada Labaru na kasar Cameroon ya bayyana damuwa kan yadda wasu iyaye daga bangaren kasar mai anfani da harshen turancin Ingilishi suke hana yaransu zuwa makaranta.

Wannan ko ya biyo bayan zanga zanga na makonni da malamai da lauyoyi suka kwashe suna yi ne, abinda ya tilasta rufemakarantu a yankin.

Ministan Isah Chiroma Bakary yace babban abin takaicin shine ta yadda ake neman salwantar da karatun yara domin wata manufa ta siyasa wannan sam bai dace da shugabannin wata rana ba.

A hirar da aka yi dashi a wannan gidan Radiyon Tchiroma yace gwamnati ba zataamince da wannan matakin ba, na iyaye su hana yaransu zuwa makaranta domin kawai wata manufar siyasa ba.

Yace “kasar gaba daya ana garkuwa da ita a hannun wasu tsirarun ‘yan siyasa, wadanda suka siyasantar da lamarin baki daya,” inji Tchiroma.

Yace munyi ALLAH waddarai da yunkurin hana shugabannin mu na gobe samun ilmin da zai basu damar daukar dawainiyar jagorantar kasar mu wata rana.

Ministan yace gwamnatin kasar dake Yaounde tana bukatar lokaci domin ta warware damuwar da ‘yan kasar dake bangaren masu amfani da turancin ingilishi suke dashi.

Kungiyoyin farar hula da shugabannin a yankin masu amfani harshen turancin Ingila na kasar suka bayyana damuwa kan abunda suka kira shirin gwamnati na tilastawa makarantuda sashen shari’a a yankin zama faransawa.

Sun bukaci zama da gwamnati a zaman wani bangare na tabbatar da cewa gwamnati ta mutunta hakkinsu kamar yadda yake cikin tsarin mulkin kasar.

XS
SM
MD
LG