Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

A Karo Na Farko Marili Daga Afirka Zai Shiga Gasar Olympics.

Wasu masu wasannin motsa jiki na Olympics.

Dan Afirka ta kudu mai gasar wasan guje-guje da tsalle-tsalle, Oscar Pistorius, shine MARILI/Maras kafa na farko daga nahiyar Afirka dake cikin wasannin Olympic na bana.

Dan Afirka ta kudu mai gasar wasan guje-guje da tsalle-tsalle, Oscar Pistorius, shine MARILI/Maras kafa na farko daga nahiyar Afirka dake cikin wasannin Olympic na bana.

Reshen hukumar dake kula da shirya wasannin na Olympics a Afirka ta a yau laraba, ya bada sanarwar cewa an zabi Oscar Pistorius, wanda gurgu ne kafafunsa biyu a yanke, wanda zai yi amfani da kafafun roba a gasar gudun tsahon mita 400 a zagayen farko, sannana yayi tseren bada sanda na mutane hudu na tsahon mita 400.

Shekarun Oscar na haihuwa 25, ana yi masa lakanin “reza maikaifin gudu” saboda amfani da robobin da yake amfani dasu wajen gudu. Yayi godiya da irin hadin kan da ake bashi domin cimma muradunsa.

Shin PI Za Ta Fashe Kuwa Ko Yaudara Ce Kawai?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG