Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

A Karo Na Uku An Sassauta Dokar Hana Zirga-ziga a Garin Kaduna


Kimanin Kwanaki uku da sake saka dokar hana zirga-zirga a garin Kaduna da kewaye, Gwamnatin jihar ta Kaduna ta sanar da sake sassauta dokar daga karfe shidda na safiya zuwa biyar na yamma a kullum.

Mai magana da yawun gwamnan jihar Kaduna, malam Samuel Aruwan ya yi Karin haske game da wannan mataki. Inda ya ce Majalisar tsaro ta jihar Kaduna ta bayar da damar fita daga karfe shida na safe zuwa karfe biyar na yamma. Ya kuma yi kira ga al’ummar jihar da su yi biyayya ga wannan umarni.

Wasu daga cikin al’umar da wannan dokar hana zirga-zirga ta ritsa da su sun koka sannan sun nuna bukatar rungumar zaman lafiya a matsayin mafita.

Sau uku kenan dai cikin mako guda gwamnatin jihar Kaduna na sanya dokar hana zirga-zirga da sassautawa biyo bayan rudanin da ya kawo guje-guje a wasu sassan jihar.

Tambayar da wasu al’uma ke yi dai ita ce, ko saka wannan doka zai iya taimakawa wajen ganin al’umar jihar Kaduna sun rungumi zaman lafiya da juna.

Domin karin bayani saurari rahotan Isah Lawal Ikara.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:31 0:00

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG