Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Gano Wani Kabari Da Aka Fara Binne Janar Alkali


Babban hafsan sojojin kasa na Najeriya, Janar Tukur Buratai (Tsakiya)

"Muna neman hadin kan duk wanda ya san inda aka sake binne gawar.” Inji babban kwamandan rundunar sojin Najeriya ta 3 Division, Manjo Janar, B. A. Akinruluyo.

Rundunar sojin Najeriya ta ce ta gano wani kabari mara zurfi inda a nan ne aka fara binne Manjo Janar Idiris Alkali mai ritaya bayan da aka kashe shi.

Jaridar yanar gizo ta Premium Times ta ce rundunar sojin ta Najeriya ta ce wadanda suka binne shi sun sake hako shi suka sake binne shi a wani wuri daban.

Amma har yanzu ba a ga inda aka sake binne shi ba.

Kabarin da aka fara binne shi, ba shi da nisa sosai daga babban titin da aka tsare shi a cewar rahotanni.

“Muna neman hadin kan duk wanda ya san inda aka sake binne gawar.” Inji babban kwamandan rundunar sojin Najeriya ta 3 Division, Manjo Janar, B. A. Akinruluyo, kamar yadda jaridar ta Premium Times ta ruwaito a yau Juma’a.

Rudunar sojin Najeriyar ta ce ta samu tabbaci daga majiyoyi hudu cewa, a wannan karamin kabarin aka fara binne mamacin, sannan hazikan karnuka masu bin diddigi su ma sun tabbatar da hakan.

A ranar 3 ga watan Satumba aka daina jin duriyar Janar Alkali a lokacin yana kan hanyarsa ta zuawa Bauchi daga Abuja.

An daina jin duriyarsa ne daga yankin Dura Du da ke karamar hukumar Jos ta Kudu a jihar Pilato.

Lamarin ya sa rundunar sojin Najeriya bin diddigin tafiyar tasa inda har ta kai ga aka gano motarsa a wani kududdufi da aka yashe a yankin.

Tun a lokacin aka kama mutum 30 bayan da sojoji suka yi wa yankin kawanya.

A ci gaba da binciken da take yi, a jiya Alhamis, rundunar ‘yan sandan jihar Pilato ta ayyana wasu mutane 8 a matsayin mutanen da ake nema ruwa a jallo ciki har da basaraken yankin.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG