Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

A Karon Farko A Borno Jama'a Zasu Yi Bikin Sallah da Walwala


Gwamnan jihar Borno Ibrahim Shettima

A karon farko cikin shekaru shida mutane zasu yi bikin sallah da walwala a jihar Borno ba tare da fargaban harin Boko Haram ba kamar yadda suka saba can baya.

Gwamnan jihar Borno Kashim Shettima a wata sanarwa da ya bayar ta kafofin labarai yace zasu bar jama'a su yi zirga zirga a lokacin bikin salla sabanin abun da suka saba ganin cikin shekaru shida da suka gabata.

Da yake zantawa da Muryar Amurka sakataren gwamnatin jihar Alhaji Usman Jidda Shuwa ya bayyana dalilin da ya sa suka dauki matakin barin mutane su yi bikin sallah cikin walwala ba tare da hanasu yin zirga-zirga ba. Yace a taron da suka yi da manyan jami'an tsaro sun amince an samu zaman lafiya yanzu ba kaman da ba. Saboda haka, zasu karfafa bincike lokacin bikin salla amma zasu bar kowa ya je inda yake so.

Yace mutane zasu iya yin yawonsu amma su lura da baki da basu sani ba. Idan sun ga haka su shaidawa jami'an tsaro. Baki na iya shigowa amma sai an bincikesu da ababen hawansu.

Ga karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:37 0:00
Shiga Kai Tsaye

Zauren VOA Hausa #EndSARS

Zauren VOA Hausa #EndSARS Kashi na Biyu 03
please wait

No media source currently available

0:00 0:18:31 0:00
Karin bayani akan #ENDSARS: Zanga Zangar Kyamar Gallazawa Al’umma Da Yan Sanda Ke Yi

Rayuwar Birni

Hira da Yusuf, wani dan asalin Jamhuriyar Nijar da ya shekara a Abuja yana sana’r gyaran takalmi
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:39 0:00
XS
SM
MD
LG