Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

A Karon Farko Al-Shabab Ta Saki Faifan Bidiyo Da Shugabanta a Ciki


Kungiyar ‘yan ta’adda ta Al Shabab a Somaliya, ta saki wani hoton bidiyo wanda a karon farko ya dan nuna shugaban kungiyar, Abu Ubaidah.

Bidiyon wanda aka sake shi a jiya Talata, ya nuna Ubaidah yana wata ganawa da mayakan Al Shabab a wani daji, gabanin wani hari da kungiyar ta kai a ranar 30 ga watan Satumba a wani filin tashin jirage da dakarun Amurka ke amfani da shi, harin da bai yi nasara ba.

Bidiyon ya nuna hannaye da kafadun shugaban na Al Shabab, amma kuma an dishe fuskarsa, yayin da aka ji muryarsa yana ba mayakan kungiyar ta Al Shabab umurnin su kaikaici ma’aikatan dakarun Amurka a harin da suke shirin kai wa.

Bidiyon har ila yau, ya nuna fuskoki da sunayen mayakan wadanda aka kai harin tare da su, amma jami’an Somaliya da na Amurka sun ce an kashe dukkan mayakan, kafin ma su kai ga ratsa filin tashin jiragen.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG