Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

A Karon Farko An Gudanar Da Allurar Rigakafin Covid-19 a Turai


A karon farko, Birtaniya ta zamanto kasa ta farko da ta gudanar da gwajin allurar rigakafin cutar coronavirus akan bil adama a nahiyar turai.

A ranar Alhamis aka yi wa wasu mutane biyu da suka amince a yi gwajin akansu allurar a birnin Oxford, inda wata tawagar kwararrun daga jami’a suka samar da rigakafin cikin kasa da wata uku.

Za dai a yi wa wasu daruruwan mutane da su ma suka mika kansu don a yi gwajin akansu, sannan za a nemo wasu mutane kwatankwacin wannan adadi, su kuma a yi musu allurar sankarau ta yadda a karshe za a gwada sakamakon gwaje-gwajen.

Amma kuma ba za a sanar da mutanen wacce allura aka yi musu ba domin a samu ingantaccen sakamako.

Idan dai har aka dace wannan gwajin allurar ya yi aiki, za a kwashe tsawon lokaci kafin kuma a hada maganin a kuma rarraba shi a sassan duniya.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG