Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

A Karon Farko Jirgi Ya Tashi Daga Isra'ila Zuwa Hadaddiyar Daular Larabawa


Hoton hanyar da jirgin ya bi

Wasu manyan tawagogin Amurka da Isira’ila, sun tashi daga filin jirgin saman Ben Gurion na kasar Isira’ila a yau dinnan Litinin, zuwa birnin Abu Dhabi, wanda shi ne karon farko da jirgin sama na wani kamfanin sufuri, ya tashi daga Isira’ila zuwa Hadaddiyar Daular Larabawa.

Jirgin saman ya bi ta sararin saman kasar Saudiyya, wanda wannan ma shi ne karon farko ga duk wani jirgin saman sufuri na kasar Isra’ila.

Tun a farkon wannan watan kasar Isira’ila da Hadaddiyar Daular Larabawa, suka amince su kulla yarjajjeniyar Diflomasiyya, tare da taimakon Amurka.

A tawagar Amurkar akwai babban mai bai wa Shugaba Donald Trump Shawara kuma surikinsa, Jared Kushner, da Mai bayar da sharawa kan tsaro na kasa Robert O’Brien, da manzon musamman kan harkokin Gabas Ta Tsakiya, Avi Berkowitz da na harkokin da su ka shafi Iran, Brian Hook.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG