Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

A Karon Farko Sabon Shugaban PNDS Ya Fita Rangadi


Shugaba Mahamadou Issoufou na Jamhuriyar Nijar, kuma na jam'iyyar PNDS Tarayya mai mulki

Sai wannan karon ne Bazoum Muhammad wanda ya gaji shugaban kasar Nijar a matsayin shugaban jam'iyyar PNDS mai mulkin kasar ya fita rangadin ganawa da magoya bayansa

Tun lokacin da Malam Bazoum Muhammad ya canji shugaban kasar Nijar Issoufou Muhammadou a matsayin shugaban PNDS mai mulki, sai wannan lokacin ne ya fita rangadin ganawa da magoya bayansa a cikin jihar Maradi.

A jawabinsa ya godewa Allah da jama'a da suka goyi bayansa kana ya yiwa masu adawa dashi da jam'iyyar shagube. Yana cewa shi ya bi hanyar gaskiya ce kodayake tana da tsawo amma ta kaiga nasara. Yace banbancinsu da 'yan adawa shi ne jagoranci nagari da Issoufou Muhammadou ya yiwa jam'iyya yake kuma yiwa kasar. Yace shugaban kasa ba dan kasuwa ba ne. Yace 'yan Nijar sun yadda dashi. Ya bada tabbacin cewa yadda shugaba Issoufou ya tanadawa jam'iyyarsa haka zai tanadawa kasar Nijar.

Wani jigo a jam'iyyar PNDS Malam Kallahu ya tofa albarkacin bakinsa. Yace ana biki koina na goyon baya da na godiya saboda aikin da gwamnatin PNDS da Issoufou Muhammadou suke yi da zuciya guda.Ya gargadi jama'a da siu cigaba da kawowa jam'iyyar mutane bisa ga ayyukan alherin da take yi.

Mata ma ba'a barsu baya ba. Shugabansu ta fito ta roki mata su fito lokacin zabe su zabi jam'iyyar domin a samu cigaba.

Ga rahoton Chaibou Mani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:46 0:00
Shiga Kai Tsaye

Laftanar Janar Farouk Yahaya

Makasan Sheikh Goni Aisami Sun Bata Sunan Sojin Najeriya – Laftanar Janar Farouk Yahaya
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:11 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Shin da gaske NNPP ba ta yi wa Shekarau adalci ba?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG