Accessibility links

Matakan Tsaro: Minista Ya Yaba Ma 'Yan Nijar

  • Ibrahim Garba

Shugaban Janhuriyar Nijar, Mahammadou Issouhou

Ganin yadda matakan tsaro ke inganta a kan iyakokin Janhuriyar Nijar, Ministan Cikin Gidan kasar ya yaba da 'yan kasar musamman ma 'yan Maradi

Ministan Harkokin Cikin Gidan Janhuriyar Nijar, Malam Hasumi Masa’udu ya yaba irin hadin kai da sauran nau’ukan gudunmowar da mutanen Maradi su ka bayar, da hakan ya taimaka wajen yakar Boko Haram da kuma kare kan iyakokin kasar. Ministan ya ce gwamnatin kasar za ta hada kai da gwamnatin Najeriya wajen duba yadda za a yaki ‘yan fashi da makami da sauran miyagun da ke addabar mutanen kan iyakar kasashen.

Wakilinmu Chaibou Mani, wanda ya aiko da wannan rahoton, ya ce cikin manyan sarakunan gargajiyan da aka gayyata har da Sultan din Tsibirin Gobir Alhaji Audu Bala Marafa, wanda ya ce, ganin abubuwan da su ka fara, lallai Janhuriyar Nijar ta ketare rijiya da baya. To amma ya ce dama idan ka ga makwabcinka na fama da wata matsala to ka yi maza ta taimaka tun abin bai iso gareka ba. Ya ce murkushe Boko Haram da aka yi a Nijar abu ne mai muhimmanci, sannan ya yi kira ga jama’a da su cigaba da ba da gudunmowa da kuma bayanan duk abubuwan da ke barazana ga tsaro.


Su kuwa talakawan da su ka hallara, kira su ka yi ga ‘yan’uwansu talakawa da su cigaba da hayar da hadin kai don kare kasarsu.

XS
SM
MD
LG