Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

A Kasar Ghana Aure daga Wata Jiha Kan Sa Dan Takara Ya Lashe Zaben Shugaban Kasa


Shugaban Ghana na Yanzu John Dramani Mahama wanda matarsa daga jihar take haka matar wanda ya gada
Shugaban Ghana na Yanzu John Dramani Mahama wanda matarsa daga jihar take haka matar wanda ya gada

Shugaban jam'iyyar NDC dake mulkin Ghana wanda ya fito daga jihar Buni Afo Mr. Okpoko Atuahi ya fada a wurin kaddamar da kundun manufofin jamiyyarsa cewa duk dan takarar da yayi aure daga jiharsa ne zai ci zaben shugaban kasar Ghana.

A jihar ce lokacin kaddamar da kemfen din neman goyon bayan al'ummar jihar shugaban kasar Ghana John Dramani Mahama ya lissafa ayyukan da gwamnatinsa zata aiwatar idan an zabeshi.

Abubuwan da zai yi sun hada da taimakawa marasa galihu da gine-gine da inganta rayuwar al'umma.

Yayinda wasu suka dauki kalamun Okpoko Atuahi da mahimmanci na cewar sai dan takara ya auri yar jiharsu kafin ya ci zabe, wasu kuma tur suka yi da kalamun.

Wani mai goyon bayan sabuwar jam'iyyar New Patriotic Party
Wani mai goyon bayan sabuwar jam'iyyar New Patriotic Party

Baba Gausu wani tsohon jamai'in tattaro jama'a na jihar ta Buni Afo a karkashin jami'iyyarsu ta NDC ya tabbatar da batun shi Mr. Atuahi. Yace tsohon shugaban kasar matarsa daga jihar ta ito. Wannan shugaban na yanzu matarsa daga jihar ta fito. Yace jihar ce kadai ta samu matan shugaba har biyu.

Jihar tana da tarihi na yanke hukumcin karshe kafin jam'iyya tayi mulki. Kawo yanzu ta jefawa shugabanni kusan ukku da suka yi mulki a kasar. Baba Gausu yace idan mutanen jihar suka ga kokarin dan takara suna mara masa baya. Idan an lura da ayyukan da shi shugaban kasan na yanzu yayi babu makawa zai sake lashe zabe, inji Baba Gausu.

Ga rahoton Baba Makeri Yakubu da karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:04:11 0:00

XS
SM
MD
LG