Accessibility links

A Kasar Mexico Mutane 36 Suka Rasa Rayukansu


Gangar jikin motar safa da ta kama wuta lokacin da ta afkawa motar daukan kaya.

Akalla mutane talatin da shida suka mutu yayin da wata mota kiya-kiya ta afkawa motar daukan kaya a kasar Mexico

Akalla mutane talatin da shidda ne suka halaka a kasar Mexico, lokacinda motar kiya-kiya da suke ciki ta apkawa wata motar dakon kaya wacce ta lalace akan hanya, motar fasinjar sai kuma ta kama da wuta.

Jami’an kasar suka ce mutane hudu sun tsallake rijiya da baya amma sun sami raunuka. Al’amarin ya auku ne a jihar Veracruz dake kudu maso gabashin kasar.

Hukumar jami’an tsaron kasar na musamman tace wadanda hadarin ya rutsa da su ‘yan kasuwa ne dake kan hanyarsu zuwa birnin Mexico daga birnin Villahermosa dake jihar Tabasco.

Shugaban kasar Enrique Pena Nieto yayi amfani da shafinsa a dandalin Twitter wajen aikawa da sakon ta’aziyya ga iyalan wadanda hadarin ya rutsa dasu.
XS
SM
MD
LG