Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gobara Ta Kashe Akalla Mutane 16 a Kasar Chile


Wani gida da gobarar daji ta cinye a garin Valparaiso, Chile ran Lahadinnan.

A wata gobara mai muni a kasar Chile akalla mutane goma sha shida suka rasa rayukansu. Idan ba'a manta ba kwanan nan kasar tayi fama da girgizar kasa.

A Chile jami’an kasar sun ce wata gobara mai tsanani ta kashe akalla mutane 16, ta kona gidaje dari biyar, a birnin Valparaiso dake kan gabar teku.

An kwashe mutane fiyeda dubu 10, ciki harda mata fursinoni su fiyeda metan a wani gidan fursina dake birnin.

Gobarar ta faro ne daga wani dan karamin daji dake kusa da gidajen marasa karfi dake kan wasu duwatsu masu yawa a birnin.

‘Yan kwana-kwana suna kokarin shawo kan gobarar, wacce iska daga tekun Pacific ke kara rurutata.

Shugabar kasar Chile Michele Bachelet, ta ayyana dokar tab baci, tuni ta tura sojoji kan titunan birnin domin tabbatar da doka da oda, da kuma hana masu kawasar ganima. Hukumomin kasar sun kafa sansanoni domin wadanda bala’in ya shafa.

Birnin Valparaiso yana daga cikin wurare da hukumar kula da harkokin ilmi da kimiyya da ala’dun gargajiya ta Majalisar Dinkin Duniya, ko UNESCO a takaice ta ayyana shi a zaman daya daga cikin wurere masu tarihi a duniya.
XS
SM
MD
LG