Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

A Legas An Rufe Wasu Gidajen da Ake Fasa Bututun Mai Ana Kwashe Man


Masu sayar da man fetur a jarka ta bayan fage

Bisa alamu gidajen goma sha biyu an ginasu ne akan hanyar da butatan mai suka bi dalili ke nan mazauna gidajen suka fasa butatan suna kwasar man fetur suna sayarwa

Gwamnatin jihar Legas ta bada umurnin rufe gidajen dake yankin Ikorodu bayan an gano ana anfani da gidajen wajen hako man fetur.

A sanarwar da gwamnatin ta bayar ta hannun kwamishanan yada labarai Mr. Steve Ayorinde ta bayyana cewa daukan matakin ya zama wajibi domin tabbatar da tsaro da kuma ceto rayukan al'umma dake cikin hatsari.

Gwamnatin jihar ta Legas tace ba zata saka ido ta ga ana yiwa tattalin arzikin kasar zagon kasa ba.

Kazalika gwamnatin ta sake bada sanarwar rufe wani otel da ta zarga da zama makafa wa masu garkuwa da mutane da kuma aikata miyagun laifuka. Tuni jami'an tsaro suka kewaye yankin da gidajen.

Gwamnati ta umurci mutanen dake zaune a yankin da su kauracewa unguwar domin gudun fadawa tarkon jami'an tsaro..

Alhaji Abdulmajjed Ali mataimakin sifeton 'yansandan Najeriya mai kula da jihohin Ogun da Legas ya tabbatar da daukan wannan matakin ta wayar tarho.

Wani Malam Abdul Kebbi yace tabbas akwai wasu da ak fitar dasu daga gidajensu domin gwamnati ta gano suna fasa bututun mai daga cikin gidajensu. Wasunsu sun fada hannun gwamnati wasu kuma sun gudu.

Ga rahoton Babangida Jibril da karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:41 0:00
Shiga Kai Tsaye

Sauyin yanayi : Yankin Sahel na Afrika

Yadda Sauyin Yanayi Ke Rura Wutar Rikici A Yankin Sahel
please wait

No media source currently available

0:00 0:12:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Nijar, Fulani, Wodaabe

Yadda Funalin Wodaabe Suka Gudanar Da Gasar Nuna Kyau A Nijar
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:22 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Gobara A Jihar New York

An Yi Jana'izar Mutane 15 Da Suka Mutu A Gobara A Jihar New York
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:00 0:00
Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG