Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Bayan Ganawa da Shugaba Buhari Babu Karin Kudin Man Fetur


Shugaban Najeriya Muhammad Buhari

Yau Talata Shugaba Muhammad Buhari ya gana da babban daraktan kamfanin mai na kasa wato NNPC, Alhaji Maikanta Baru domin yin nazari akan halin da samar da mai da kuma rarraba mai yake gudana a kasar da kuma tattauna irin matakan da gwamnati ya kamata ta dauka domin inganta sha'anin raba mai.

Bayan ganawar babban daraktan Alhaji Baru ya bayyanawa manema labaru cewa babu wani shirin kara kudin mai sabanin irin labarun da aka dinga yayatawa a kafofin labaru ta yanar gizo.

Ya sake nanatawa cewa gwamnatin Buhari bata da niyyar kara kudin farashin man fetur yanzu ko a nan gaba.

Shi ma babban sakataren 'yan kasuwa masu hada hadar man fetur Alhaji Danladi Fasali yace ko su basu da niyyar kara farashin man fetur. Yace kwai babbar alama cewa za'a rage farashin man saboda suna ta kawo kaya. Yace yanzu dai an kurewa man fetur farashi.

Alhaji Fasali yace a shirin da su keyi idan kayansu na gaba suka iso zasu sayar dasu kasa da farashen gwamnati. Ko yanzu ma akwai wasu 'yan kasuwa dake sayar da man kasa da farashen gwamnati. A Legas akwai wani kamfani dake sayarwa dari da talatin da daya maimakon dari da arba'in da biyar. Yace kudin kara sauka ya keyi ba wai yana karuwa ba ne.

Ga rahoton Umar Faruk da karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:32 0:00

An Sami Karuwar Farashin Kayayyaki A Jamhuriyar Nijar
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:42 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
Shiye-Shiryen Shiga Watan Azumi A Kasar Ghana
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:56 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
Ziyarar Sakatare Blinken A Jamhuriyar Nijar
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:57 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
Al'umomi Sun Koka Game Da Tashin Farashin Kayayyaki
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:57 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG