Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

A Libya An Kama Mahaifin Wanda Ya Kai Harin Manchester


Jami’an tsaro a kasar Libya sunce sun kama dan uwa da kuma mahaifin Salman Abedi mutumin daya kai harin kunar bakin wake a birnin Manchester.

Mai magana da yawun rundunar dakile ta’adanci ta kasar yace kwanan nan Hashim Abedi ya zanta da dan uwan nasa kuma ya san shirye shiryen da yake yi na kai harin. Haka kuma sunce suna da shedar cewa da shi da dan uwan nasa suna da alaka da kungiyar IS.

Suma ‘yan sandan Ingila sun kama karin mutane guda biyu jiya Laraba. An kama wata mace a lokacin da suka kai sumame wani gida a arewacin Mancester. Mutum na biyu kuma an kama shi ne a garin Nuneaton dake tsakiyar Ingila.

Haka kuma akwai wasu mutum biyar da aka kama dangane da harin. To amma ‘yan sanda basu bada wani bayani akan ko kila suna da hannu a harin ba.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG