‘Yar Majalisar Dokokin Jahar Bauci mai wakiltar Dass, Hajiya Maryam Garba Bagel, ta ce lura da marayu da marasa galihu nauyi ne da ya rataya a wuyar Ma’aikatar Mata ta jaha a jahohin Najeriya, amma ba wata hukuma ba.
Hajiya Maryam Bagel, wadda ke cikin wani rukunin ‘yan Majalisar Dokokin jahar ta Bauci da ke ziyarar aiki a nan Amurka, ta ce a jahar Bauchi an kirkiro wata hukuma ta kula da marayu, don haka sai ta dauke wannan nauyin daga wuyar Ma’aikatar Mata, wadda kuma ba ta da wata dangantaka da hukumar kula da yaran. Ta ce idan ana wani muhimmin abu na marayu, Ma’aikatar Mata ake kira amma ba wannan hukumar da aka kirkiro daga baya ba; amma kuma ba a ba da cikakken ikon yin wani abu ga shashin kula da yara da marayu na Ma’aikatar ta Mata. Don haka bayan halarta taron sai kawai a kasa yin wani abu. Ga shi kuma ba a baiwa hukumar kula da yaran ikon zuwa taron ba, don haka sai a kasa samun wanda zai yi wani abu saboda wannan rudamin.
Sannan kuma akan cire ma ma’aikatan gwamnati kashi daya bisa dari (1%); mayan jami’an gwamnati kuma kashi biyu bisa dari (2%) ta yadda adadin abin da ake cirewa kan kai Naira mliyan 28 duk lokacin da aka yi albashi tun bayan kafa wannan hukumar a 2012. To amma tun lokacin da aka kafa wannan hukumar zuwa yau babu wasu yaran da hukumar ta taimaka masu saboda wannan matsalar. Shi ya sa ake ganin cire wannan kudi bai yi amfani ba – amma ba wai taimaka ma yaran ne bai da muhimmanci ba.
Don haka kamata ya yi a koma kan tsarin da aka saba da shi saboda matasa da marayun su amfana a maimakon halin da aka shiga na rudami:
Ga cikakken bayanin da ta yi a hirarsu da abokin aikinmu Ibrahim Alfa Ahmed: