Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

A na Barazanar Korar Gwamnan Adamawa


Shugaban Najeriya kuma shugaban jam'iyyar PDP

A na barazanar korar gwamnan Adamawa, Murta Nyaka daga jam'iyyar PDP

A jihar Adamawa PDP bangaren Bamanga Tukur na barazanar korar gwamnan jihar Murta Nyako daga jam'iyyar.

A wani taron manema labarai da bangaren Bamanga Tukur suka kira sun ce ya zama wajibi su dauki matakin korar gwamnan jihar Murta Nyako daga jam'iyyarsu ta PDP domin take-taken gwamnan da masu goyon bayansa na neman canza sheka zuwa wata jam'iyyar.

Bayan gwamnan wadanda barazanar ta shafa har da mataimakinsa Barrister Bala Ngilari da 'yan majalisar dokoki da shugabannin kananan hukumomi da wasu kusoshin jam'iyyar. Sakataren bangaren Bamanga Tukur ya ce su ba zasu yarda su bar wadanda aka zabesu a karkashin PDP su rika anfani da mukaminsu da kudin PDP suna cin zarafin jam'iyyar. Maimakon su yiwa talaka aiki sai suna yiwa jam'iyya zagon kasa. Ta dalilin haka ya zama wajibi su dauki matakan fatartakarsu daga jam'iyyar.

A nasu martani da suka mayar shugabannin PDP 'yan bangaren Kugama dake dasawa da gwamna Nyako sun yi fatali da barazanar suna cewa kuararin haramtattun shugabanni ne domin haka basu da matsaya ko madogara.Sun kara da cewa ba'a zabesu ba kuma haka rahoton Sule Lamido ya nuna.

Shi kuma gwamna Murtala Nyako ya ce yana nan daram cikin jam'iyyar PDP.

Ga rahoton Abdulawahab Mohammed.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:15 0:00
Shiga Kai Tsaye

Shin PI Za Ta Fashe Kuwa Ko Yaudara Ce Kawai?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG