Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Majalisar Wakilan Najeriya Ta Yiwa Kundun Tsari Gyarar Fuska


Sojoji suna tsaro lokacin zaben kasa a Najeriya

Majalisar Wakilan Najeriya Ta Yiwa Kundun Tsarin mulkin kasar garanbawul abun da majalisar dattawan kasar ta kasa yi.

A zaman majalisar wakilan Najeriya da ya kaisu har cikin dare sun yiwa kundun tsarin mulkin kasar garambawul, abun da majalisar dattawa ta kasa yi.

Yayin da majalisar ke zamanta kungiyoyi daban daban dake fafitikar kare hakkin dan adam da goyon bayan kungiyar kwadago ta kasar suka taru a gaban majalisar suna zanga-zangar lumana. A bayanin da suka yi kungiyoyin sun ce sun zo ne su nuna rashin amincewarsu da matsayin majalisar dattawa inda ta yi watsi da baiwa kananan hukumomi hakkin cin gashin kansu ta sake jaddada barin kudadensu karkashin gwamnatocinsu ta kuma ki ta cire rigar kariya ta shugaban kasa da gwamnoni.

Da alamu dai gangamin da kungiyoyin suka yi ya sa hakonsu ya cimma ruwa domin yan majalisar wakilan sun kai har dare suna zama har sai da suka cimma kada kuri'u game da abubuwa da suke so a gyara a kundun tsarin mulkin kasar. Abubuwan da suka amince a yi masu garambawul sun hada da baiwa kananan hukumomi cin gashin kansu, da cire rigar kariya a kan sugaban kasa da gwamnoni da kuma rushe hukumomin zabe na jihohi.

Kafin 'yan majalisar su fara zamansu akwai raderadin cewa wasu gwamnoni sun gana da wasu 'yan majalisar a bayan fagge. To amma sai gashi sun juyawa gwamnonin baya.Su 'yan majalisar sun ce sun yi hakan ne domin talakawa da suka zabesu suke yiwa aiki ba gwamnoni ba. Abubuwan da suka gyara abubuwa ne da suka shafi rayuwar dan adam da jin dadin jama'a da kuma cigaban dimokradiya.

Da aka jawo hankalin 'yan majalisar cewa duk abubuwan da suka amince dasu abubuwa ne da majalisar dattawa ta yi watsi da su. Sai suka ce majalisar dattawa ta basu kunya domin a yadda ake tafiya yanzu majalisun jihohi da kananan hukumomi su ne suke shan wahala. Babu zabe mai adalci a jihohi na kananan hukumoni kana kariyar da gwamnoni ke da shi ta sa su aikata zalunci da satar biliyoyin kudi duk a rasa yadda za'a yi da mutum domin yana da kariya. Irin wannan cin zarafin bil adam dole ne a kawai da shi.

Madina Dauda nada rahoto.

please wait

No media source currently available

0:00 0:05:30 0:00
Shiga Kai Tsaye

Shin PI Za Ta Fashe Kuwa Ko Yaudara Ce Kawai?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG