Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

A Nahiyar Afirka Najeriya Zata Zama Kasar da Masu Saka Jari Suka Fi So - Buhari


Shugaba Muhammadu Buhari

Jiya Talata a Faransa Shugaba Buhari yace manufar sauye sauyen da gwamnatinsa keyi yanzu shi ne karfafa wa masu saka jari gwiwa da basu tabbacin karfin tattalin arzikin kasar.

Yayinda yake yiwa 'yan kasuwa jawabi a hedkwatar Movement of the Enterprise of France ko MEDEF a takaice, Shugaba Buhari ya sake jaddada kudurn gwamnatinsa na yaki da cin hanci da rashawa.

Yace "sauye sauyen da mu keyi yanzu soboda sake baiwa masu saka jari tabbaci ne da kuma toshe duk wata hanya ta barna da almubazaranci da dukiyar jama'a. Mun kuma maida hankali akan kwato kudade da dukiyoyi kasar da aka sace"-inji Shugaba Buhari lokacin da yake jawabi a dandalin Najeriya da Faransa na saka jari.

Shugaban yace gwamnatinsa zata yi duk iyakacin kokarinta ta tabbatar kasar ce ta daya da masu saka jari zasu fi so su saka jari a nahiyar Afirka.

Yace mun kama hanyar bunkasa da yawalta saboda kasar nada albarkatu a fannin noma da ma'adanan kasa da kwararrarun ma'aikata da babbar kasuwa idan aka yi la'akari da yawan jama'ar kasar. Akwai hada hadar kasuwanci bisa ga manufofin saka jari masu kyau da ingantattun dokoki dake iya tabbatar da abubuwan da ka iya faruwa a fannin kasuwanci.

Inji Buhari kasar nada albarkatu da yawa banda na man fetur kuma mun dukufa mu inganta masana'antu da fadada su da nufin bude wasu fannonin tattalin arzikin kasa.

Da ya juya kan sayar da hannun jarin kamfanonin gwamnati da gwamnatocin da suka shude suka soma yi sai shugaban yace za'a cigaba da yin hakan tare da shigo da wasu kamfanonin amma komi za'a yi a bayyane. Ba za'a yi rufa rufa ba kamar yadda aka gani can baya.

Mun gane cewa 'yan kasuwa masu zaman kansu 'yan gida da na waje dake kasuwanci a kasar su ne gimshikin gina da habaka tattalin arziki saboda haka zamu rungumesu mu kuma basu duk taimakon da suke bukata, inji Shugaba Buhari

Shugaba Buhari yace zamu cike gibin da aka samu wurin gina abubuwan dake taimakawa tattalin arziki saboda a kirkiro ayyukan yi da habaka jari da ingiza habakar tattalin arziki yadda kowa zai samu wadata a kasar.

Da yake mayarda martani shugaban MEDEF Pierre Gattaz yace kungiyar mai mambobi 800,000 da suka hada da masana'antu masu sarafa kaya da 'yan kasuwa zasu shirya su kai ziyara Najeriya wata mai zuwa. Mr Gattaz yace tawagar da zata Najeriya zata hada da masu son saka jari a fannonin noma da hakar ma'adanai da kira motoci da makamashi da horas da kwarararru da sarafa abinci da sufuri da dai sauransu.

XS
SM
MD
LG