Accessibility links

A Najeriya Shubannin Addini Sun Yaba da Dokar Hana Auren Jinsi Daya


Dan luadi da tutar 'yan madigo da luadi

Yayin da gwamnatocin kasashen yammacin turai da Amurka ke cigaba da sukar gwamnatin Najeriya kan dokar hana auren jinsi daya shugabannin addini na kasar yabawa suke yi

Yayin da dokar hana luadi da madigo da auren jinsi daya da gwamnatin Najeriya ta aiwatar ke cigaba da jawo ma kasar suka daga gwamnatocin kasashen yammacin turai da Amurka da ma kungiyoyin kare hakin dan adam har da Majalisar Dinkin Duniya, su ko shugabannin addin na kasar yabawa suka yi.

Mai magana da yawun shugabannin addini a taron da suka yi ya ce dailin taron shi ne su nuna godiyarsu dangane da yadda majalisun dokokin Najeriya da gwamnatin tarayya suka kafa dokar hana madigo da luadi da auren jinsi daya. Ya ce a matsayinsu na shugabannin addini suna godiya kwarai da gaske. Ya ce nasara ya zo Najeriya ya zauna har shekaru sittin amma wannan shegantakar bai yi ba har ya tafi. Sabili da haka ba zasu yadda ba da wasu su kawo masu wasu abubuwan da addininsu da al'adunsu basu amince da su ba. Hakika 'yan majalisu da gwamnati sun yi abun kirki kuma hakan ya kamata ko kuma ya zama dole su yi domin ana yin dimokradiya ne.

A tsarin dimokradiya wadanda suka fi rinjaye su ne da murya. Ya ce a Muslunci addini ya hana mace ta auri mace ko namuji ya auri namuji ko a yi luadi ko madigo. Kiristoci ma suna da addini wanda bai yadda a yi luadi ba ko madigo ko kuma auren jinsi daya. Ya ce a Najeriya Musulmai da Kiristoci ke da kasar. Duk wanda ba Musulmi ko Kirista ba yana cikin tsirarun mutane kuma bashi da wata murya.

Wadanda suke yin madigo ko luadi ba za'a kirasu 'yan adam ba domin dabbobi ma basa yin madigo ko luadi.Taure ba zai bi taure ya yi masa barbara ba. Haka akuya bata bin akuya ta yi barbara.Kaza bata bin kaza ta yi mata barbara. Zakara baya bin zakara ya yi masa barbara. Haka ma jaki ba zai bi jaki ba ya yi masa barbara. Tun da dabbobi basa yin wannan abu to wadanda suke yi suna kasa da dabbobi. Sabili da haka basa cikin lissafin mutane, wato basa cikin mutane.

Wadanda suka ga su rayuwar yin luadi da madigo zasu yi sai su je wata kasar daban su cigaba da yi. Amma a Najeriya yin luadi ko madigo karya doka ne kuma akwai hukumci. A najeriya jama'ar Musulmi addininsu da mutuncinsu bai yadda ba haka ma Kiristoci addininsu da mutuncinsu bai yadda ba. Wadan nan al'ummomin biyu su ne jama'ar Najeriya.

Dangane da hukumci babu kisa domin gwamnatin tarayya bata yadda ba. Hukumcin yin bulala da tara a ke yankewa. Babu wanda aka kashe. Wadanda suke yin luadi a tambayesu maza biyu suka haifesu? Wadanda kuma suke yin madigo mata biyu suka haifesu ko yaya?

Ga karin bayani.

XS
SM
MD
LG