Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

A Nijer, Wani Shiri Da Obama Ya Bullo Da Shi Ya Yaye Dalibai Kan Dabarun Kafa Masana'antu Da Shugabanci


Foto Achiv: Ansyen Prezidan Etazuni Barack Obama

Daliban Cibiyar Koyon Dabarun Kafa Masana'antu da Koyon Shugabanci kimanin 45 ne aka yaye a Jamhuriyar Nijer a wannan zangon a karkashin shirin da tsohon Shugaban Amurka Barack Obama ya bullo da shi don ciyar da kasashen Afurka gaba.

Ofishin jakdancin Amurka a jamhuriyar Nijer ya yaye wasu matasa kimanin 45 wadanda suka kammala daukan horon watanni 3 akan dubarun kafa masana'antu da shugabancin harakokin jama'a, kamar yadda aka saba a karkashin shirin tsohon shugaban Amurka Barack Obama

Gomman matasan da su ka fito daga sassan Nijer ne suka sami wannan horo a karkashin shirin YALI na shugaba Barack Obama, wanda aka gudanar a tsawon makwanni inda kwararu daga jami’oin Amurka suka bada darusan da suka shafi sha’anin kafa masana’antu da hikiomin tafiyar da su da kuma yadda ake shugabancin harakokin jama’a.

Moussa Chehou na daga cikin wadanda suka sami takardar shaidar lakantar wannan fanni a yayin wani kwaryakwaryan bukin da aka shirya a cibiyar raya al’adun Amurka, kuma ya tofa albarkacin bakinsa a hira da muryar Amurka, ya na mai tabbatar da fa'idar wannan shirin.
Sabanin yadda ake tattara matasa kasar Amurka ko birnin Dakar na Senegal domin samun irin wannan horo a bana abubuwa sun gudana ne ta yanar gizo sanadiyar anobar covid 19 Kuma a cewar magatardar kungiyar matasan YALI Marichatou Samira Amadou an sami nasarori fiye da yadda ake zato.

Daga lokacin bullo da shirin shugaba Barack Obama a 2010 kawo yau daruruwan matasan Nijer suka ci moriyar wannan tsari mai hangen baiwa matasan Afrika damar bada gudunmowa a aiyukan ci gaban wannan nahiya ta yadda zasu ba da misalai ga kannunsu kwatankwacin bajintar da aka gani a wajen wasu daga cikin shugabanin da suka gabata wadanda komai nasu ya tahallaka akan maganar fitar wannan nahiya daga ramin da tsinci kanta ciki.

Saurari rahoton Suleiman Barma:

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:51 0:00


XS
SM
MD
LG