Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Masanan Kasashen Afrika Sun Fara Taron Nazarin Mafitar Illolin Canjin Yanayi


A yayinda ake wuni na 2 na taron sauyin yanayi a birnin Glasgow na kasar Birtaniyya wasu kwararu daga jami’oin kasashen Sahel sun fara gudanar da taro a jamhuriyar Nijer.

Wannan na zuwa ne domin nazarin wani rahoton bincike akan dalilan dake haddasa canjin a wannan yankin wanda akasarin jama’arsa ke dogaro da ayyukan noma da kiwo.

Illolin canjin yanayi abubuwa ne da ake ganinsu a fili karara a kasashen yankin Sahel shekaru da dama inda a kulliyaumin bayanai ke nunin gara jiya da yau saboda yadda wannan al’amari ke shafar rayuwar jama’a ta yau da kullum a dauka daga fannin noma da kiwo sana’ar kamun kifi da dai sauransu. Dalili kenan masana daga jami’oin kasashen Afrika da jami’an cibiyoyin bincike suka hallara a birnin Yamai domin nazarin mafita.

Bayanai sun yi nunin da cewa sama da million 50 na mazaunan kasashen Sahel da na kudancin Sahara na dogara ne akan ayyukan kiwo, sai dai sannu a hankali illolin canjin yanayi sun jefa wadanan mutane cikin halin karancin abinci da matsanancin talauci inji ministan ilimi mai zurfin Nijer Mamoudou Djibo a yayin da ya ke jawabin bude wannan taron inda ya kuma kara da gargadi mahalaran sun kula da wannan babban kalubale.

Yace wannan manuniya ce ga masu aikin bincike su hada karfi da sauran bangarori domin zurfafa bincike don samar da mafita ga fannin noma da kiwo da ke matsayin babbar madogara ga jama’a sakamakon cikas da canjin yanayi ya haddasa.

A ranar alhamis ne ake kammala wannan taro da zai tsayar da mahimman shawarwarin da a karshen za a gabatarwa shuwagabanin kasashen yankin sahel don ganin an dauki matakan da suka dace da illolin canjin yanayi tun wuri bai kure ba.

Saurari cikakken rahoton a cikin sauti:

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:00 0:00

Dubi ra’ayoyi

Ana ci gaba da muhawara a kan ko daga wane yanki na Najeriya yakamata shugaban kasar na gaba ya fito

Karin bayani akan Bidiyo

Sabbin kotunan soji a Maiduguri za su yi shari’a ga kanana da manyan sojoji

Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Zabarmawa, Zabuwa, Ghana

Yadda Aka Gudanar Da Wasan Zabuwa A Ghana
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:14 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Aminu Saira

Aminu Saira
please wait
Embed

No media source currently available

0:00 0:04:33 0:00
Karin bayani akan Nishadi
XS
SM
MD
LG