Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

A Saliyo Matasa Sun Kaiwa Jami'an Kiwon Lafiya Hari A Kusa Da Freetown


Titunan birnin Freetown suna nan shall babu kowa sakamakon dokar hana fita domin yaki d a cutar Ebola.

A Saliyo jami’an kasar sun ce wasu matasa sun kaiwa jami’an kiwon lafya hari yayinda suke binne mutane da suka mutu sakamakon kamuwa da suka yi da cutar Ebola. Al’amrin ya auku ne kusa da Fretown babban birnin kasar.

Arangamar ta auku ne jiya Asabar a rana ta biyu da fara aiki da dokar hana fita da gwanati ta kafa da zummar dakile yaduwar cutar wacce ta kashe fiyeda mutane dubu biyu da dari shida a yammacin Afirka.

Maharan suka sun waste bayan da ‘Yansanda suka turo da Karin jami’ai domin bada kariya ga masu aikin jana’izar.

Saliyo ta umarci ‘yan kasar su kusan milyan shida su zauna gida na kwanaki uku yayinda jami’an kiwon lafiya suke kokarin gano wadanda suka kamu da cutar, sannan su wayar da kan sauran jam’a kan hanyoyin d a zasu kare kansu daga kamua da cutar.

Cutar Ebola ta kama mutane fiyeda dubu biyar da dari uku galibinsu a Laberiya, da saliyo da kuma Guninea, kuma bata nuna alamar lafawa ba. Haka nan ma cutar da bulla a kasashen Najeriya da Senegal.

XS
SM
MD
LG