Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

A Sudan ta Kudu Gwamnati Da 'Yan Adawa Sun Rabbata Hannu Akan Yarjejeniyar Zaman Lafiya


Shugaban Sudan ta Kudu Salva Kiir da Riek Machar yayinda suke rabbata hannu akan yarjejeniyar da suka cimma jiya, Agusta 05, 2018 a Khartoum.
Shugaban Sudan ta Kudu Salva Kiir da Riek Machar yayinda suke rabbata hannu akan yarjejeniyar da suka cimma jiya, Agusta 05, 2018 a Khartoum.

Shugaba Salva Kiir na Sudan ta Kudu da madugun 'yan adawa Riek Machar sun rabbata hannu akan yarjejeniyar zaman lafiya wadda ta kawo karshen yakin basasan da suka kwashe shekaru biyar suna yi wanda kuma ya lakume dubban rayuka tare da raba miliyoyi da muhallansu

Jiya Lahadi, bangarorin kasar Sudan ta Kudu da basa ga maciji da juna suka sanya hannu akan wata yarjejeniyar samun zaman lafiya, a yunkurin baya bayan nan na kawo karshen yakin basasar shekaru biyar daya kashe dubban mutane da kuma sa miliyoyin mutane rasa matsugunansu.

Kamfanin dilancin labarun kasar da ake kira SUNA a takaice, ya bada labarin cewa shugaba Salva Kiir da tsohon mataimakin sa, shugaban yan tawaye Riek Machar ne suka rattaba hannu akan yarjejeniyar.

Wani bangaren yarjejeniyar ya tanadi, shugaba Kir yaci gaba da zama shugaban kasa, kuma Macha ya koma kasar a zaman mataimakin shugaban kasa na farko cikin mataimakan shugaban kasa guda biyar.

Za’a yi watani takwas a zaman watanin kafa harsashen mulki na wucin gadi. Bayan haka za’a tsawaita mulkin wucin gadin na wasu na shekaru uku. Majalisar Ministoci zata kunshi minstoci ashirin daga jam’iyar shugaba Kir, tara daga bangaren Macha, sa’anan shidda daga sauran bangarorin

Wannan shine yunkuri na baya bayan nan na kulla yarjejeniyar samun zaman lafiya da tsagaita wuta, tun lokacin da yaki ya barke a shekara ta dubu biyu da goma sha uku.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG