Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

A Syria Hari kan Ofishin 'Yansanda Ya Rutsa da Mutane 16


Yadda ofishin 'yansandan Syrian ya zama bayana harin
Yadda ofishin 'yansandan Syrian ya zama bayana harin

Wani harin tagwayen bama-bamai kan ofishin 'yansandan Syria yayi sanadiyar mutuwar mutane 16

Sama da mutane 16 ne aka bada rahotan sun rasa rayukansu a wani hari da aka kaiwa ofishin ‘yan sanda da tagwayen bama-bamai a Damascus, babban birnin Syria.

Ministan cikin gidan Syria, Laftanan-Janar Mohammad al-Shaar, ya fadawa manema labarai cewa wasu da ya kira “‘yan ta’adda” ne suka kaiwa ofishin ‘yan sanda hari da bama-bamai a unguwar al-Midan dake birnin Damacus a jiya Litinin, kafin ‘daya daga cikinsu ya tayar da nakiya ya kashe kansa.

Shi kuma ‘daya maharin ya kutsa cikin harabar ginin ‘yan sandan, inda suka harbe shi har Lahira, abinda kuma yayi sanadiyar tashin bam din dake jikinsa.

A cewar kungiyar “Observatory” dake saka ido kan harkokin cin zarafin bil Adama a Syriada mazauninta ke Birtaniya, mutane 11 ne suka mutu, cikinsu har da ‘yan sanda da kuma fararen hula.

Ya zuwa yanzu dai babu wani mutum ko kungiya da suka fito suka dauki alhakin kai wannan hari.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG