Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

A Thailand Bom Ya Kashe Sojojin Kasar Hudu


Firayim Ministan Thailand Prayut Chan-ocha

Thailand ta dade tana fama da tashin hankali a kudancin kasar inda bom ya tashi a gefen hanya ya hallaka sojoji hudu

‘Yan sandan kasar Thailand sunce wani bom da ya tarwatse a gefen hanya a yankin kudancin kasar da ake fama da tashin hankali ya kashe sojoji hudu.

Hukumomi sun ce wadansu sojoji da kuma farin kaya sunji rauni a fashewar da ta auku yau jumma’a a lardin Pattani.

Lardin dake kan iyaka da galibi Musulmi ne yana fama da tashin hankali yayinda mayakan kabilar Malay suke yakar gwamnatin Thailand da mabiya addinin Buda suka fi rinjaye a yunkurin neman Karin ikon cin gashin kai.

Nan da nan babu wanda ya dauki alhakin fashewar.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG