Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

A Tona Asirin Wadanda Suka Kashe Shugaba Baare Mainasara, A’a Bai Dace Ba.


APTOPIX Niger Elections
APTOPIX Niger Elections

Wasu ‘yan Niger sun Bayyana raayin su game da ko ya dace a tona wadanda suka kashe tsohon shugaban kasar Niger Baare Mainasara ko kuma a’a.

Yayin da wasu ke cewa hakan yayi dai-dai wau kuma na cewa aci gaba da barin al’amarin ga ALLAH.

Wakilin sashen Hausa Sule Mummuni Barma ya jiwo raayin wasu ‘yan kasar game da wannan batu.

Ga dai wasu daga cikin wadan da suka bayyana raayoyin su.

‘’Sunana Mallam Ibrahim a raayi na ni dan kasa ni a nawa raayin so nake yi a kara bincike aga shin dawa-dawa nene suka yi wannan kashin gillan ga Ibrahim Baare Mainasara, abinda yasa nace haka shine naga mu kasa ce ta demokaradiyya bai kamata ace azo a kashe shugaban kasa haka nan kumawadanda suka kashe shi an san da suna nan kuma shugabanni daban-daban sai suce za ayi bincike akan wannan kashin amma har yanzu ba abinda aka yi’’

Ita ma wannan baiwar ALLAH mai suna Ramatu ga abinda take cewa.

‘’Gaskiya wannansharaa kamata yayi a bar wa ALLAH tunda wannan abu anyi shi yau shekaru 17 ba ayi sharaa ba to a yaushe za ayi sharaa.’’

Ga dai Sule Mummuni Barma da sauran masu bayyana raayoyin su 2’28

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:28 0:00
Shiga Kai Tsaye

Hawan Nasarawa, jihar Kano a Najeriya, lokacin da aka gudanar da bukukuwan Sallar Eid el Fitr
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG