Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

A Tsohuwar Gwamnatin Da Ta Gabata An Sace Dala Miliyan 15 - inji Osinbajo


Professor Yemi Osinbajo
Professor Yemi Osinbajo

Mataimakin shugaban kasar Najeriya yace gwamnatin da ta gabata ta sace Dala Miliyan Dubu Goma sha Biyar na talakawa ta wajen badakalar sayen makamai.

Mataimakin shugaban kasar Yemi Osinbajo ya fada yau talata cewa, an yi asarar kudin ne ta cin hanci da rashawa,karkashin shirin sayen makamai na gwamnatin tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan.

Shugaban kasa mai ci yanzu Muhammadu Buhari ya lashe zabe bara da alkawarin cewa zai shawo kan matsalar cin hanci da rashawa. Sai dai shugaban kasar yace satar da aka yi zamanin mulkin Jonathan ta bar baitulmalin kasar wayam.

Tunda ya hau karagar mulki a watan Mayu, an kama jami’an tsohuwar gwamnati da dama bisa zargin cin hanci da rashawa, da suka hada da tsohon mai ba shugaban kasar shawarwari kan harkokin tsaro Sambo Dasuki.

A cikin watan Janairu, ministan watsa labarai na Najeriya yace jami’an gwamnati hamsin da biyar, da kuma ‘yan kasuwa sun sace dala miliyan dubu shida da saba’in na talakawa tsakanin shekara ta dubu biyu da shida zuwa dubu biyu da goma sha uku.

Mataimakin shugaban kasar ya fada yau Talata cewa, babu wani jami’in gwamnatin da zai yi tsammani cewa, zai wawuri dukiyar kasa ya kwana lafiya.

XS
SM
MD
LG