Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

A Watan Fabrairun 2022 Za a Yi Babban Taron APC na Kasa


APC
APC

Jam’iyyar APC mai mulki ta sanar da cewa a watan Fabrairun 2022 za a yi babban taronta na kasa.

Shugaban kungiyar gwamnoni da ake kira PGF kuma gwamnan jihar Kebbi, Atiku Bagudu shi ne ya bayyana hakan bayan wata ganawa da shugaba Muhammadu Buhari.

Gwamna Bagudu ya sami rakiyar shugaban rikon jam’iyyar APC ta kasa Mai Mala Buni, da gwamnan jihar Jigawa Abubakar Badaru zuwa fadar shugaban Najeriya.

Ya fada wa manema labarai cewa an yi taron ne don yi wa shugaba Buhari bayani game da shawarar da kungiyar gwamnonin ta yanke bayan wata ganawa da maraicen jiya Lahadi.

A cewar Bagudu, gwamnonin sun cimma matsayar za a yi taron a watan Fabarairun shekarar 2022 haka kuma aka gabatar da kudurin ga shugaban kasa.

XS
SM
MD
LG