Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaba Buhari Yayi Wa Iyalin Rabaran Dr Obiora Ezekiel Ta’aziyya


Rabaran Dr. Obiora Ezezkiel, shugaban majami’ar Christian Pentecostal Mission a Legas ko CPM a takaice ya rasu.

A cewar wasu majiyoyi, a jiya Lahadi a lokacin sujjada aka sanar da mutuwar babban sanannen rabaran din.

Haka kuma mawakiyar bishara Judikay ta tabbatar da rasuwar a shafinta na Insragram.

Shugaba Muhammadu Buhari ya ya yi wa al’ummar kristocin Najeriya gaisuwar rashin Rabaran Ezekiel yana mai cewa abubuwan da ya yi zasu ci gaba da yin tasiri.

Ranar Lahadi shugaba Buhari ya ambaci karfin ruhaniyar Ezekiel da kuma yadda ya koyar da wasu da yawa yayin da ya bukaci a yi addu’o’i don matarsa Rabaran Mercy da sauran iyalanta.

XS
SM
MD
LG