Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

A yau laraba za a fara shari’ar tsohon madugun sojojin kabilar Sabiyawan Bosniya, Ratko Mladic, a wata kotun Majalisar Dinkin Duniya inda zai fuskanci tuhume-tuhume har 11.


Tsohon kwamandan Sabiyawa Ratko Mladic, lokacinda ya bayyana gaban kotun kasa kasa dake bin kadun rikicin Yugoslavia.

Ana zargin tsohon kwamandan sojojin sabiyawan mai shekaru 70 da haihuwa da laifin bayar da umurnin kashe Musulmi dubu 8, dukkansu mazaje manya da yara, a garin Srebrenica na Bosniya.

A yau laraba za a fara shari’ar tsohon madugun sojojin kabilar Sabiyawan Bosniya, Ratko Mladic, a wata kotun Majalisar Dinkin Duniya inda zai fuskanci tuhume-tuhume har 11, ciki har da kisan kare dangi, da laifuffukan yaki da cin zarafin bil Adama.

Ana zargin tsohon kwamandan sojojin sabiyawan mai shekaru 70 da haihuwa da laifin bayar da umurnin kashe Musulmi dubu 8, dukkansu mazaje manya da yara, a garin Srebrenica na Bosniya, da kuma yin kofar rago domin kai farmaki ba kakkautawa a kan Sarajevo, babban birnin kasar.

Mladic ya samu horaswa a makarantar sojoji ta tsohuwar Yugoslaviya a Belgrade. A lokacin da kasar ta fara rarrabewa a farkon shekarun 1990, ya samu karin girma ya zamo kwamandan dukkan sojojin kabilar Sabiyawan Bosniya wadanda suka fara yakar sauran jinsunan kasar domin ware gefe guda ma kabilar Sabiyawa.

An yi kisan kare dangi na Srebrenica a 1995 lokacin da dubban fararen hula suka taru a yankin da aka ayyana a zaman tudun mun tsira na MDD, amma sojojin Sabiyawa sun yi watsi da wannan suka tattara mazaje dubu 8, suka hallaka su baki daya. Daga bisani an gano manyan ramukan da aka yi ta zuba gawarwakin mutanen.

An kama Mladic a watan Mayun bara, kusan shekaru uku a bayan da aka damke shugaban Sabiyawan Bosniya na zamanin yaki Radovan Karadzic. Kwararru suka ce lallai Mladic ya samu goyon bayan sojoji da hukumomin leken asirin kasar Serbia ta yadda har aka yi shekaru masu yawa ana farautarsa babu labari.

Shin PI Za Ta Fashe Kuwa Ko Yaudara Ce Kawai?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG