Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, ya yi Allah wadai da sabbin hare-haren da suka yi sanadiyyar mutuwar mutum akalla 30 a karamar hukumar Batsari da ke jihar Katsina.
Hare-haren, wadanda rundunar ‘yan sandan jihar ta tabbatar, an kai su ne a kauyukan Tsanwa da Damkal.
“Shugaban Najeriya ya yi Allah wadai da jerin hare-haren da mahara suka kai kan manoma a kauyukan Damkal da Tsanwa a karamar hukumar Batsari,” kamar yadda kakakinsa Garba Shehu ya wallafa a shafinsa na Twitter a yau Lahadi.
Buhari ya kara da cewa, “ba za mu lamunci kisan mutane a matsayin daukar fansa ba.”
Shugaban Najeriyar, wanda ya jajintawa al’umar yankunan, ya kuma nuna muhimmancin bari hukumomi su yi bincike “tare da daukan matakan da suka dace.”
Kamar yadda kafofin yada labaran kasar suka ruwaito, wasu ‘yan bindiga ne suka kashe mutum 21 a Tsauwa kana suka halaka wasu tara a Danga a karshen makon da ya gabata.
Jaridun Najeriya da dama sun ruwaito kakakin ‘yan sandan jihar ta katsina, Gambo Isah yana cewa, “mafi aksarin wadanda aka kashe dattawa ne da yara kanana da suka kasa tserewa maharan.”
Bayanai sun kuma yi nuni da cewa ‘yan bindigar sun far wa kauyukan ne a kan Babura.
‘Yan sanda sun ce an kama daya daga cikin maharan hade da babura tara.
Katsina, jihar da shugaban na Najeriya ya fito, ta sha fama da matsalar hare-haren ‘yan bindiga da masu satar shanu, wadanda sukan far wa kauyukan sassan jihar a duk loakcin da suke so.
Hukumomin jihar da na tarayya kan yi ikrarin cewa sun kama ko kashe ‘yan bindigar da dama, amma duk da haka ba a daina kai hare-haren ba.
A wasu lokuta a baya, har sulhu an yi da ‘yan bindigar, a kokarin da gwamnatin jihar ta Katsina ke yi na shawo kan matsalar.
Za ku iya son wannan ma
-
Fabrairu 26, 2021
Tattaunawar Gumi Da 'Yan Ta'adda Ba Alheri Ba Ne - Dattawan Arewa
-
Fabrairu 26, 2021
Fulani ‘Yan Bindiga Ba Barayi Ba Ne – Sheikh Ahmed Gumi
-
Fabrairu 26, 2021
Masu Fataucin Abinci Da Dabbobi Sun Shiga Yajin Aiki A Najeriya
-
Fabrairu 26, 2021
Ba Mu Da Abincin Da Zamu Ciyar Da 'Yan Makarantar Kagara- ‘Yan Bindiga
-
Fabrairu 25, 2021
Yadda Aka Kama Jabun Magunguna A Jihar Kano Na Sama Da N150M