Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Nada Sabon Sarkin Gombe


Bukin Nada Sabon Sarkin Gombe

An nada Abubakar Shehu Abubakar a matsayin sabon sarkin Gombe, biyo bayan rasuwar Sarki Shehu Usman Abubakar a makon jiya.

Abubakar Shehu Abubakar dan shekaru 36 ne wanda shine karami daga cikin 'ya'yan marigayi Sarki Shehu Usman Abubakar wanda ya rasu a Ingila, a makon da ya wuce.

Juma'ar nan ne aka nada wannan sabon sarki, wanda zai jagoranci masarautar Gombe, dake arewa maso gabashin Najeriya.
XS
SM
MD
LG