Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Abubuwan Da Kudurin Dokar Hana Janareta a Najeriya Ya Kunsa


Hoton janareta

A jiya ne Majalisar Wakilai a Najeriya ta gabatar da kudurin wata doka wacce za ta hana amfani da kuma sayar da janareta a duk fadin kasar.

Sanata Muhammad Enagi Bima na jihar Niger ne ya mika kudurin dokar, wanda ya ce manufar dokar ita ce a taimaka wajen bunkasa fannin wutar lantarki a Najeriya.

A yanzu dai kudurin dokar ya samu wuce karatu na daya.

Ya kuma kara da cewa akwai bukatar a kawo karshen illolin da amfani da janareta ke janyowa ga rayuwar al’umma da kuma muhalli.

Dokar dai ba za ta shafi wasu wurare ba, kamar asibitoci da filin jiragen sama da na kasa, da dai duk wani wurin da al’umma ke yawan zuwa mai bukatar wuta sosai.

Dokar za ta kuma bada izinin a rufe duk wanda ya shigo da janareta cikin Najeriya ko kuma ya sayar da ita.

Za a rufe duk wanda aka kama da wannan laifin a gidan yari na tsawon shekara 10.


Tuni dai lamarin ya fara janyo ce-ce ku-ce kan shafukan sada zumunta duba da yadda ake yawaita amfani da janareta a Najeriyar wacce ta yi shekara da shekaru tana fama da rashin ingantacciyar wutar lantarki.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG