Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Abubuwan Da Shugaba Buhari Ya Fada a Jawabinsa Kan Coronavirus


Shugaba Muhammadu Buhari
Shugaba Muhammadu Buhari

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya gabatar da jawabi da yammacin jiya, inda ya bayar da umurnin dakatar da zirga-zirga na tsawon mako biyu a Abuja, Legas da kuma Ogun don rigakafin cutar Coronavirus.

Wannan umarnin dai zai fara aiki ne daga ranar 30 ga watan maris, da karfe 11 na dare.

Shugaban ya jaddada cewa dukkannin mutanen da ke zaune a wadannan wuraren, ya zama tilas su zauna a gida kuma a dakatar da tafiya zuwa ko kuma dawowa daga biranen.

A jawabin nasa, shugaban ya ce gwamnatinsa za ta tura tallafi ga jama’ar da ke kewayen manyan biranen da rashin fitowar zai shafa.

Duk da haka shugaban ya ce masu gudanar da muhimman ayyuka irin jami’an tsaro, masu aikin lantarki, man fetur, raba abinci da ‘yan jarida ka iya cigaba da gudanar da harkokinsu ba tare da matsala ba.

Amma ‘yan jaridan sai sun bayar da kwakkwarar hujjar cewa ba za su iya aiki daga gida ba.

Kazalika shugaban ya bayyana cewa za a samar wa ‘yan gudun hijira da ke sansanonin gudun hijira kayayyakin abinci da zai iya ciyar da su na tsawon watanni biyu.

Jiragen sama ma an dakatar da tashinsu, in dai ba ta kama ba.

Ya ce ya amince da matakan da jihohi ke dauka na takaita zirga-zirga a tsakanin jihohi ko manyan birane.

Shugaban ya jaddada yadda har yanzu cutar bata da magani, kuma babban abin da zai taimaka a yanzu shi ne zama a gida da kuma rage cudanya da mutane.

Ya kuma ce za a bai wa al’ummomin da ke kusa da biranen da aka takaita zirga-zirga kayayyakin agaji, duba da yadda matakin zai shafi rayuwarsu ta yau da kullun.

A cewar shugaban, ya san wadannan matakan zai sanya ‘yan Najeriya da dama cikin matsi, amma wannan lamarin ya shafi rai da mutuwa, saboda haka dole a dauki matakan.

Ya zuwa yanzu dai mutum 111 ne ke dauke da cutar ta Coronavirus a kasar Najeriya.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG