Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Abuja: Gobara Ta Tashi a Ma’aikatar Ilimi


Wani gini da ya kama da wuta a jahar Legas, Najeriya

Wata gobara da ba a tantance musabbabin ta ba, ta tashi a shelkwatar ofishin ma’aikatar ilimi da ke Abuja.

Rahotanni sun ce an ga ma’aikatan kashe gobara suna ta fadi tashin kashe wutar wacce ta mamaye hawa na shida inda daga nan ne aka ce wutar ta samo asali, daga baya kuma har ta shafi hawa na bakwai.

An kuma ga ma’aikatan wurin suna ta arcewa domin neman mafaka daga wutar yayinda hayaki ke tashi a sama.

Akwai bayanai da ke cewa duk kayayyakin kashe wuta a ma’aikatar sun lalace wadanda aka ajiye domin bacin rana.

Sai dai rahotannin baya baya nan sun ce an kashe gobarar kuma al’amura sun fara komawa yadda suke a da yayin da ake kokarin tantance abinda ya haddasa wutar.

Koda yake wakilin Muryar Amurka da ke Abuja, ya ce bayanan da ya tattara na nuni da cewa wutar ta fara ne saboda hadewar waoyiyin wutar lantarki a daya daga cikin ofishin ma’aikatar.

XS
SM
MD
LG