Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

ABUJA: Shugabannin Addini Na Jerin Gwanon Matsawa Gwamnati Akan 'Yan Matan Chibok


Shaikh Nuru Khalid cikin farar riga da Bishop John Onayekan ta hannun dama a jerin gwanon kungiyar BBOG domin kwato 'yan matan Chibok

Shugabannin addini sun shiga jerin macin da 'yan kungiyar dake fafutikar sako 'yan matan Chibok wato, Bring Back Our Girls ko BBOG suka shirya na cika shekaru uku da sace 'yan makarantar mata dake Chibok da 'yan Boko Haram suka sace

Inji 'yan kungiyar BBG gwamnatin Najeriya ta ba 'yan kasar kunya kan yadda take tafiyar da lamarin ceto 'yan matan Chibok da yanzu suka kwashe shekaru uku a hannun 'yan ta'addan da aka ce an tarwatsa sansaninsu dake dajin Sambisa.

'Yan kungiyar BBOG da shugabannin addini a jerin gwanon kwato 'yan matan Chibok da suka rage a tsare
'Yan kungiyar BBOG da shugabannin addini a jerin gwanon kwato 'yan matan Chibok da suka rage a tsare

Kungiyar tace a wannan makon suke yunkurin matsa lamba domin a ceto sauran 'yan matan, suna mai cewa ya isa haka nan domin babu sauran bada uzuri kan cetosu.

Sakatariyar BBOG Aishatu Yusuf tana mai cewa "a dawo mana da 'yan matan a raye"

Shekaru uku da suka gabata aka sace 'yan matan su 245 amma yanzu ana neman 195 da ba'a san inda suke ba. Tace basa son su maimata yukurin domin shekaru uku dogon lokaci ne.

Mataimakin shugaban al'ummar Chibok dake zaune a Abuja yace abun mamaki ne a ce 'yan kasa sun rike wasu 'yan kasa kuma har yanzu ba'a san inda suke ba kuma gwamnati tana ji tana gani.

Kungiyar tana tambaya cewa tunda aka tarwatsa 'yan ta'addan daga dajin Sambisa to a ina 'yan matan suke. Shin sun mutu ne ko suna raye.

Yayinda 'yan kungiyar BBOG ke maci a Unity Fountain shugaban darikar Katolika Bishop Onayekan da Limamin Masallacin Unguwar 'Yan Majalisa Nuru Khalid sun shiga jerin gwanon suna kara jan hankalin gwamnati ta kara dagewa kan gano sauran 'yan matan. Sun ce basu raina kokarin gwamnatin ba zuwa yanzu da ta cimma nasarar lafar da babbar fitinar Boko Haram da kuma samun dawowa da wasu cikin 'yan matan.

Bishop John Onayekan da Shaikh Nuru Khalid sun ce suna fatan kalubale dake damun kasar zai kawar nan gaba saboda 'yan ta'addan Boko Haram ba addinin Musulunci suke wakilta ba.

Ministan tsaron Najeriya Mansur Dan Ali ya kara bada tabbacin yin duk abun dake yi wuwa wajen gano sauran 'yan matan da kuma danko madugun 'yan ta'addan da suka sace matan, wato Abubakar Shekau.

Kungiyar BBOG tace ba zata daina fafutika ba har sai an gano sauran 'yan matan ko gawarwakinsu.

Ga rahoton Nasiru Adamu El-Hikaya da karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:55 0:00

Facebook Forum

Laftanar Janar Farouk Yahaya

Makasan Sheikh Goni Aisami Sun Bata Sunan Sojin Najeriya – Laftanar Janar Farouk Yahaya
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:11 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Shin da gaske NNPP ba ta yi wa Shekarau adalci ba?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG