Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Abun Da Zai Tabbatar Da Dimokuradiyya Da Zaman Lafiya Shi Ne Ganin An Yi Adalci Ga Duk Mai Neman Takara - Dikko Radda


Katsina state governorship aspirant, Umar Dikko Radda.
Katsina state governorship aspirant, Umar Dikko Radda.

Mai neman takarar gwamna a jihar Katsina kuma tsohon shugaban hukumar bunkasa kanana da matsakaitan sana’o’i ta Najeriya SMEDAN, Dakta Dikko Umar Radda, ya bayyana cewa adalci ga duk mai neman takara a zaben fida gwani ne kawai zai tabbatar da dorewar dimokuradiyya da zaman lafiya a siyasar kasar.

Dakta Radda ya bayyana hakan ne a wata hira ta musamman da muryar Amurka a birnin tarayyar kasar Abuja a daidai lokacin da ake tunkarar zaben fidda gwanin jam’iyyun siyasar Najeriya ciki har da jam’iyyar APC mai mulki da babbar jam’iyyar adawa ta PDP a Najeriya,.

Ya na mai yin kira da uwar jam’iyyar APC da sauran shuwagabanninta su tabbatar da cewa an yiwa duk mai neman takara adalci.

A yayin amsa tambayoyi a game da kudurorin da yake da su ga jihar Katsina da ya ke neman takarar gwamna a cikinta, Dakta Dikko Radda ya ce zai mayar da hankali kan muhimman abubuwa da suka hada da neman bakin zare ga matsalolin tsaro da suka addabi jama’ar jihar, ya na mai cewa ba ci gaban da za’a samu sai an yi maganin tsaro ta hanyar yin amfani da mutanen dake zama a yankunan karkara da aka fi fama da su domin tabbatar da su shiga a dama da su doń kawo zaman lafiya mai dorewa.

Sai kuma bangaren noma wanda shi ne ginshikin tattalin arziki, sai bangaren samar da aikin yi ta hanyar kafa hukumar kanana da matsakaitan masana’antu a Katsina domin ganin an bada tallafin da ya kamata ga masu kanana da matsakaitan masana’antu, sai bangaren kiwon lafiya, ilimi da dai sauransu.

Rahotanni daga jihar Katsina sun yi nuni da cewa ‘yan siyasa 9 ne ke neman takarar gwamna a jihar kuma dukkan mutanen 9 sun sami damar sayan fom din nuna sha’awa da tsayawa takara tare da cika wa’adin mika fom din da aka kammala.

Haka kuma, wasu majiyoyi sun yi nuni da cewa kowanne mai neman takarar na dakon amincewar gwamnan jihar mai ci wato, Aminu Bello Masari, sai dai gwamnan wanda uban gida ne ga yawancin masu neman takara a jam’iyyar ta APC bai ce uffan ba a game da mai neman takarar da zai iya ba wa goyon baya ba.

A halin yanzu dai, wadanda suka gabatar da fom dinsu ga jam’iyya tare da gabatar da dalilansu na ganin sun cancanta su sami tikitin jam’iyyar APC mai mulkin jihar sun hada da mataimakin gwamnan jihar, Mannir Yakubu, tsohon sakataren gwamnatin jihar, Mustapha Muhammed Inuwa, da tsohon kwamishinan kasafi da tsare-tsare na jihar, Faruk Lawal Jobe.

Sauran sun hada da tsohon babban daraktar bankin dake kula da yadda yan kasa zasu mallaki muhalli wato mortgage bank na Najeriya, Ahmed Musa Dangiwa, tsohon babban daraktar kamfanin buga da sabunta kudi na Najeriya wato NSPMC, Abbas Umar masanawa, sai babban daraktar hukumar kula da kananan da matsakaitan masana’antu ta Najeriya wato SMEDAN, Dakta Umar Dikko Radda.

Sai kuma wadanda ke neman goyon bayan wakilan jam’iyyar domin samun tikitin takarar jam’iyyar ta APC da suka hada da tsohon babban jami’in tsaro CPSO ga shugaba Muhammadu Buhari, Abdulkarim Dauda Daura, sanata Abubakar Sadiq Yar’Adua, da Umar Abdullahi Tauri Tata.

Abun jira a gani shi ne yadda zabukan fidda gwanin jam’iyyun siyasar Najeriya zasu gudana a karshen watan Mayun.

A saurari bayani cikin sauti:

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:46 0:00

Hawan Nasarawa, jihar Kano a Najeriya, lokacin da aka gudanar da bukukuwan Sallar Eid el Fitr
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG