Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Adadin Masu Coronavirus a Amurka Ya Haura Miliyan 1


Adadin wadanda suka kamu da cutar coronavirus a Amurka ya cika miliyan daya duk da cewa jihohi da yawa na daukar matakan bude harkokin kasuwancinsu a hankali.

Bisa ga wata kididdiga daga jami’ar Johns Hopkins, miliyan 1 adadi ne mafi yawa ga kowacce kasa a duniya, yayin da adadin wadanda suka kamu da cutar a fadin duniya ya zarta miliyan 3.

Sama da Amurkawa 57, 000 sun mutu sanadiyyar cutar coronavirus.

Wata kididigar kuma daga kamfanin dillancin labaran Reuters ta ce cutar coronavirus ta kashe Amurkawa kusan 2,000 a duk rana a watan Afrilu.

Wasu jami’an kiwon lafiya a Amurka sun yi imanin cewa ta yi wu takamaiman adadin Amurkawa da suka kamu da cutar ya fi wanda aka sani saboda rashin gwaji da kuma sanar da yawansu.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG